A jihar Kano: Autan Bawo ya jagoranci addu’o’in zaman lafiya

A jihar Kano: Autan Bawo ya jagoranci addu’o’in zaman lafiya

Autan Bawo ya jagoranci addu’o’in zaman lafiya

Tura wannan Sakon

DAGA Abubakar Garba Isa

A makon da ya gabata ne Maimartaba sarkin Rano, Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa (Autan Bawo) ya gabatar da taron saukar karatun Al-kura’ani da addu’oin neman zaman lafiya ga qasa da jihar Kano musamman Rano.

Da yake jawabi, limamin shugaban Malaman Rano, Asheik Wada Sunusi Rano ya yi addu’a ga maimarta sarki bisa qoqarinsa na addu o’in da yake yawan yi wa Nijeriya da jihar Kano a koda yaushe.

A jawbinsa, maimartaba sarkin Rano, Alhaji Muhammad Kabiru Inuwa ya gode wa gwamnan Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje wurin tsaurara matakan tsaro a jihar. Taron ya sami halartar hakimai da dagatai da limaman masarautar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *