A jihar Kano: Hukuma kashe gobara ta ceci rayuka fiye da 111

PFO Sa, eed Muhammad Ibrahim

PFO Sa, eed Muhammad Ibrahim

Tura wannan Sakon

Daga Muhammad Mustapha Abdullahi

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta yi hobbasa a watan Fabrairu karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Hassan Ahmad Mu­hammad.

Kamar yadda mai yawunta PFO Sa’eed Muhammad Ibrahim ya bayyana cewa, hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta samu kiraye- kiraye da da ma a cikin watan da ya gabata na Fabrairu daga tashoshinta da suke birnin da ka­uyukan jihar Kano guda 27.

Sa’eed Muhammad ya ce, sun samu kira na kashe gobara kimanin 95 sai kira na neman agaji 59 da kira wanda suke cewa, na tsokana ko na karya wanda shi ma ya kai kimanin guda 13 , baya ga dukiyar da aka rasa sakamakon hatsar­urruka na gobara da suka faru wadda ta kai Naira miliyan 11,325,000 sai duki­yar da aka ceta da ta kai Naira miliyan 180,278,000 sai kuma rayuka da aka rasa guda 8 da wadanda aka ceta guda 111.

Sa, eed Muhammad ya kara da cewa a wani labarin kuma sun samu kira daga titin unity road da ke kasuwar kanti kwari a birnin Kano da misalin karfe 4:25 na yamma ta bakin wani bawan Allah mai suna Salisu Mu’azu inda tuni jami’an mu suka isa wajen suka samu wuta ce ta kama, wanda kuma cikin ikon Allah sun samu damar shawo kanta, sun kashe ta ba tare da wani asarar rai ko jikkata ba..

Sa’eed Muhammad ya ce hukumar kashe gobara ta hijar Kano na amfani da wannan damar wajen kira ga Al, umma da su rinka kiyaye yadda suke amfani da wuta domin kare kai daga gobara da hatsarurruka da suke faruwa akan tituna domin kare lafiyarsu da dukiyarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *