A jihar Kano: Masu laifuffuka 331 sun fada komar ‘yan-sanda

hukumar Yan sanda

hukumar Yan sanda

Tura wannan Sakon

Rabiu Sanusi Daga Kano

Fiye da mutane 331 ne ‘yan sandan jihar Kano ta yi nasarar yin awon gaba da su kan laifuffuka mabambamta a jihar cikin makonni hudu. Hakan na zuwa lokacin da sabon Kwamishinan ‘yan-sandan jihar, CP Abubakar Lawal Daura lokacin da yake gabatar wa da manema labarai masu laifin karo na farko bayan shafe makonni biyu da zuwansa matsayin Kwamishinan ‘yan-sanda a jihar Kano.

CP Abubakar Lawal ya ce, cikin ikon Allah ana ci gaba da samu nasara daga batun samar da zaman lafiya a jihar Kano ta kokarin gwamnati jihar, kwamitocin unguwanninsu kan bangaren ‘yan-sanda da masu hannu da shuni da masaratu da sauran jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, inda ya yaba da irin gudunmuwar da ‘yan jarida suke bayar wa da ma sauran bangarori yana ba su nasara.

Daura ya ce, wadanda aka kama sun hada da ‘yan fashi da makami 51 da ‘yan damfara 12 da masu garkuwa da mutane domin kudin fansa 69 da masu safarar mutane mutum 7. Sauran masu laifufukan sun hada da masu satar motoci da baburan Adaidaita Sahu su 18 sai ‘yan daba guda 168, haka kuma ‘yansandan sun yi nasarar kama wadanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi su 6. Kazalika, an kuma kubutar da mutune 11 daga hannun masu garkuwa da mutane da kuma mutanen da a kai safara zuwa bautarwa wadansu kasashen aikatau su 17.

An kuma gano bindigogi kira daban-daban har guda 48 da motoci 24 da Adaidaita Sahu 12 da babura guda 2 sai wukake guda 94, akwai kuma tabar wiwi dauri 306 da katan din kwayar turamol guda 2. Akwai kuma batiran motoci guda 30 da aka gano tare da plasma tb guda daya, sai fankar sama guda 9, da injin markade guda daya, sai sholisho guda 48, akwai kuma kwayar edol guda (1,2143) sai wayar hannu 75 da abin balle karfe kowane iri da kuma tarin master keys. Daga karshe, kwamishinan ‘yan sandan ya yi kira ga jama’ar jihar Kano da su ci gaba da taimkon jami’an tsaro wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali fadin jihar Kano dama kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *