A jihar Kano: Mata suna kara rungumar PRP -Habiba Bello

PRPLogo
Alhussain daga Kano
Maza da mata musamman matasa a jihar Kano, alamu sun nuna suna kara rungumar jam’iyyar PRP, wanda idan aka lura abin ba haka yake ba a shekarun baya.
Wannan na faruwa ne sakamakon wayar da kai da ake yi lokaci zuwa lokaci a kan manufofin jam’iyyar. Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugabar mata ta jam’iyyar da ke jihar Kano, Hajiya Habiba Bello Abdullahi , a lokacin da take zantawa da manema labarai .
Hajiya Habiba Bello Abdullai, ta ce, domin ganin PRP ta sami nasara a zaben shekarar 2023, jam’iyyar tana shirya taro lokaci zuwa lokaci a daukacin kananan hukumomin jihar 44, inda ta ce, nan gaba kadan jam’iyyar za ta raba wa mata kayan tallafin koyon sana’o’i daban-daban domin su dogara da kansu.
Ta kara da cewa, babu shakka mata suna da rawar da suke takawa sosai a fagen siyasar jihar da ma ta kasa baki daya, shi ya sa jam’iyyar take bai wa mata kima da kuma kulawa ta musamman .
Ta kuma jawo hankulan matan da cewa, ranar zabe su tabbatar sun kada wa PRP kuri’unsu, sannan su zabi cancanta ba mayaudara ba.