A Jihar Yobe: Kwalara ta halaka mutane 3

Kwalara ta halaka mutane 3
Sani Gazas Chinade Daga Damaturu
Akalla mutane 3 suka rasa rayukansu yayin da wadansu mutane 2 ke kwance a gadon asibiti sakamakon barkewar cutar kwalara a karamar hukumar Jakusko ta jihar Yobe cikin makon da ya gabata.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin Babban Sakataren Hukumar Lafiya a Matakin Farko na jihar Yobe, Dokta Babagana Kundi a jawabinsa ga manema labarai a garin Damaturu.
Babban sakataren ya tabbatar da cewa, jin labarin hakan ya sa hukumarsa ba ta yi kasa a gwiwa ba, suka gaggauta tura wata tawagar gaggawa ta kwararru a yankin domin shawo kan cutar gudin kar ta bazu.
A cewarsa tunin an shawo kan lamarin, kuma “na yi magana da shugaban tsare-tsare na cibiyar lafiya, inda na umurce shi da ya fara feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka a yankin nan take ba tare da jinkiri ba domin gudun ci gaba da yaduwar annobar ta mai Baushe (Kwalara).
A nasa jawabin dangane da barkewar cutar ta kwalara a karamar hukumarsa, shugaban karamar hukumar Jakusko, Alhaji Abdullahi Hassan Gwayo, jan hankalin jami’an kiwon lafiyar da su dauki matakan gaggawa domin kare yaduwar cutar a wannan yanki da ma dukkan sassan jihar baki daya kasancewar cuta ce matukar hadarin gaske da kan iya yaduwa babu kakkautawa da zarar an yi sakacin daukar mataki.
Shugaban ya kuma shawarci al’ummar da ke yankin da su dukufa wajen daukar matakin tsabtace muhallinsu, musamman wajen tsabtace abin sha da abincinsu da sauran mu’amullarsu.