A Jos: An bude gasar musabaka karo na 35

A Jos: An bude gasar musabaka karo na 35

A Jos: An bude gasar musabaka karo na 35

Tura wannan Sakon

Daga Mohammed Ahmed Baba Jos

A ranar Lahadi da ta gabata ne aka gudanar da taron musabakar Al-kur ani a dakin taro na Jama’atu  bayan dalibai sun gabatar da karatun Al-kur ani, shugaban taron kuma  babban Malamin garin Jos, Sheikh Lawal Adam ya bude taro da addu’a da kuma gode wa Allah da sake zagayowar musabakar.

Bayanin shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa, Alhaji Shehu Bala Usman, ya yi godiya ga masu shirya taron tsawon shekaru 35, sannan ya bayar da gudunmawar Naira dubu 100 shi da kansilolinsa.

Sai jawabin Alhaji Ibrahim Ibzar shugaban kamfanin madaba’ar Ibzar Ya ce, shekaru 35 masu albarka ne tun daga matakin karamar hukuma da jiha da kuma tarayya, ya kara da cewa, bayar da kyautar mota ko kudi suna gushewa yanzu kamata ya yi a dinga biya wa yara karatu a sami wani kos da zai amfani al’umma.

Daya daga cikin masu shirya gasar, Sheikh Aminu Sadis ya yi godiya na ganin musabakar karo na 35, ya ce, kullum al’umma tana bukatar tallafi na daukar nauyin karatun dalibai,sannan ya yi ta’aziyyar wadansu ‘yan kwamitin musabakar da suka rasu,bayan nan an gabatar da alkalai da masu taimaka masu.

 Sai jawabin Muhammad Adam Al-Kadi wanda Barista Sani ya wakilta, inda ya bayar da gudunmawar Naira dubu 5, shi ma Sheikh Khalid Usman Khalid ya ce, kafin a fara musabaka irin wannan akwai masu rubuta Al-kur’ani da alkalami da tawada, idan sun rubuta shafi daya sai sun jira ya bushe sannan su rubuta dayan ba tare da sun manta ko wasali daya ba.

Shi ma Dokta Nazifi Yunus Daraktan makarantar Al-bayan ya ce, kamar shekaru 25 da suka gabata, idan ya zo yana zama ne a baya, amma yanzu su ne suke zama a kujerun manyan baki bayan rasuwar malamai da manyan gari da suke zama a gurin, wanda kujeru ne da suke da zafi.

Sai nasiha daga Sheikh Muktar Adam Al-bahari in da ya ce, babbar rahamar da Allah ya bai wa dan’Adam shi ne, Alkur’ani duk wanda ya same shi ya sami nutsuwa, Sarkin Narkuta, Injiniya Muhammad Bello, shi ma ya sanya albarka inda ya bukaci a kimsawa dalibai tsoron Allah da son juna.

Alhaji Idriss Kwando ya yi kira ga dalibai a kan su daina mayar da hankali kan kyautar da ake ba su kawai, kuma dukkansu masu nasara ne, sai mai gabatar da bayani a gurin, Sheikh Abdurrahman Rayyan inda ya ce, babu wata ni’ima da Allah ya yi wa dan’Adam kamar Alkur’ani shi ne littafi mafi girma da aka bai wa manzo mafi girma.

Daga karshe, sai jawabin godiya daga sakataren hukumar Alhazai, Barista Auwal Abdullahi, daga nan aka rufe taron da addu’a ana yin karatun safe da yamma ne, a sati mai zuwa za’a rufe gasar inda ta kunshi rukunin maza da mata, kamar yadda aka sabayi duk shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *