A Jos: An bude musabakar Al-Kur’ani ta jiha, karo na 35

Mohammed Ahmed Baba daga Jos
An gudanar da bude gasar Alkur’ani ne a ranar Lahadin da ta gabata a babban dakin taro na Jama’atul Nasril Islam da ke babban Masallacin Juma’a na garin Jos.
Babban limamin garin Sheikh Lawal Adam shi ya bude taron da addu’a, mai jawabi na gaba shi ne Sheikh Aminu Sadis wanda ya yi maraba da baki sannan Ayuba Kwade wanda ya wakilci Sheikh Abdul’Aziz Yusuf.
Shugaban gidauniyar Musabaka ta jihar Filato ya bayayana cewa, ana gudanar da gasar ne bisa matakai hudu akwai na karamar hukuma wanda aka yi kwanan baya sannan na jiha da za a yi yanzu sai na Tarayya, daga karshe sai gasar Al’kur’ani ta duniya.
Jawabin Malam balarabe Abdullahi, wanda shi ne mai tattaro bayanai na ci gaba da aka samu a harkokin Musabaka ya ce, an fara gasar ne tun a shekara ta 1986 inda jihar Filato ta shiga a 1987 kuma shigar farko ta zo ta hudu ya kara da cewa, kungiyar Jama’atul Nasril Islam ce ta dauki nauyin kudin motar dalibai da masaukinsu a lokacin.
Ya ce bana sun sami wakilcin kananan hukumomi 12 a cikin guda 17, ya ce inda a lokacin da ake yawan samun rikici a jihar ba ya wuce kananan hukumomi 4 ake samu.
Sai babban malami mai jawabi a taron Sheikh Mukhtar Adam Al-bahari, ya bayyana muhimmacin Alkur’ani sannan ya ce shi ne babbar Mu’ujizar Manzon Allah SAW.
Ya ja hankalin dalibai da su dinga hada karatun addini da na boko, wani malami shi ma ya tofa albarkacin bakinsa mai suna Malam Sulaiman Ahmed limamin masallacin Sultan Bello da ke Kaduna ya yi albishir cewa, yanzu haka an bude Jami’ar karantar da Alkur’ani ta yanar gizo inda inda daga karshe aka karrama wannan malami da lambar yabo ta hannun mai tallafa wa gasar duk shekara.
Muhammad Adam Alkadi inda ya tallafa da Naira milliyan1.5 sannan daga karshe sai wani mai suna Alhaji Ibrahim Ibzar inda ya tallafa wa alkalan da Naira dubu N50,000 kowanen su, sannan a sati mai zuwa za a rufe gasar wacce ake yin ta cikin sati daya.