A Jos: Fitiyanul Islam ta yi taron Maulidi karo na 42

Daga Mohammed Ahmed Baba Jos
Kungiyar Fitiyanul Islam reshen jihar Filato, ta gudanar da taron maulidi karo na 42 a garin Jos, bayan fara taron Khalifa Mustapha Aliyu Gwarando shi ne ya karanta tarihin haihuwar Annabi S A W.
Shi ma Sheikh Muktar Adam Al-bahari ya yi jawabi a kan ma’anar sunan Ahmadu shi ne abin da ake gode wa shi kuma Muhammad abin godiya Mahmud wanda kowa ya gode wa ya kara da cewa, su ‘yan Tijjaniya suna girmama kowa, ko daga ina kake, sannan kungiyar Lajna ta bai wa shugaban Fitiyanu lambar yabo.
Daya daga cikin ‘yan kwamitin maulidin, Abubakar Atiku Yusuf, ya yi jawabin godiya ga wadanda suke tallafa masu.
Shi ma Injiniya Mansur Salihu na Kande ya yaba da yadda tsarin taron yake tafiya ya ce”wannan karon duk shugabannin kungiyar sun halartaci taron.