A Kaduna: Isa Ashiru ya gabatar da takardun karatunsa a kotu

A Kaduna: Isa Ashiru ya gabatar da takardun karatunsa a kotu

Isa Ashiru

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

A ranar Alhamis da ta gabata, tsohon dan TAKARAR Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar [ PDP ] Alhaji Isa Ashiru Kudan ya amsa kiran babbar kotun jihar Kaduna da mawauninta ke Dogarawa a Zariya, inda wani mai suna Abdullahi Isa ya shigar karar neman tsohon dan takarar gwamnan da aka ambata da ya gabatar da takardun shaidar karatunsa a gaban wannan kotu.

Da ya ke Magana a gaban babban shari’a a wannan kotun da aka ambata, Abdullahi Isa da ya gabatar da wannan karar ya shaida wa kotun cewar, ya yanke shawarar kai wannan karar ce domin kawo karshen batutuwan da ake yada wa cewar, Alhaji Isa Ashiru, takardun bogi ya mallaka ba ingantatrtu ba.

Bayan dogon turanci a tsakanin lauyan wanda ya shigar da karar da kuma lauyan Alhaji Isa Ashiru Kudan, Kotu ta karvi takardun karatu na Alhaji Isa Ashiru Kudan, daga nan kuma mai shari’a Kabiru Dado ya dage sauraron karar har zuwa ranar 27 ga wannan wata na Afirilun shekara shekara ta 2022.

Bayan fitowa daga cikin kotun, Alhaji Isa Ashiru Kudan ya shaida wa manema labarai cewar, ko kadan bai mamakin kais hi kara a wannan kotu kan wannan batu na rashin ingancin takardun karatunsa ba, a cewarsa ‘yan siyasa babu abin da ba za su yi ba, musamman in sun hango haske ga duk wani dan siyasar da ya shiga gabansu.

Alhaji Isa ya ci gaba da cewar, duk wani dan siyasa ya na da kyau ya tanadi ire – iren wadannan bita – da – kullin siyasa da wasu suke kullawa da a ganinsu, shi ne babbar hanyar da za su bi, domin cimma burinsu na son mulki ko ta halin kaka a wannan lokaci kakar zaven shekara ta 2023.

Da kuma ya juya ga ‘yan siyasar da suke da ire – iren wadannan halaye da su tuna cewar ‘’ shi fa mugunta, fitsarin fako ne’’, ga duk mai shirya ko wane irin kutulkwilar siyasa ga wani dan siyasa, shi ma ya tanadi lokacin da za a yi ma sa kila ma fiye da abin da yay i wa wani ko kuma wasu.

Sai dai kuma Alhaji Isa Ashiru ya tabbatar da cewar, jawo akalarsa zuwa kotu a kan takardun karatunsa, kaimi aka yi ma say a kara tashi tsaye, domin fuskantar kalu – balen da za su ci gaba da tasowa a kan burinsa na mai neman jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar gwamna a zaven shekara ta 2023, a cewarsa, alamu nasara ya ke gani, ba wata ko kuma wasu matsaloli ba.

A karshen ganawarsa da wakilinmu Alhaji Isa Ashiru Kudan ya shawarci daukacin maoya bayan jam’iyyar PDP da kuma ma su wukar – yankar Magana na wannan jam’iyya su fahimmanci hada kai da kuma tunanin makomar jam’iyyar a shekara ta 2023 su ne manyan abubuwanda ya dace su sa a gabansu, ba wasu abubuwa da za su kawo matsala ga jam Iyyar ko kuma wani dan takara da zai tsaya takara a zaven shekara ta 2923 ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *