A Kaduna: Muradin Uba Sani, ciyar da harkokin mata, matasa -Hajiya Sharifat

Senator Uba Sani
An yi kira ga al’ummar yankunan Samunaka da ke karamar hukumar Lere a jihar Kaduna da su fito kwansu da kwarkwatarsu ranar zaben gwmnoni domin zabar Sanata Uba Sani, dan takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar apc bisa kwarewarsa a sha’anin siyasa, da kudirin ciyar da harkokin mata da matasa baki daya.
Bayanin kiran ya fito ne daga bakin wata ‘yar gwagwarmaya kan sha’anin siyasar yau da kullum, daga yankin karamar hukumar Lere, Hajiya Sharifat Muhammad, ita ce ta bukachi hakan yayin ganawarta da manema labarai ranar Alhamis din makon da ya gabata.
Hajiya sharifat ta ce, zabar Sanata Uba Sani a matsayin gwamnan jihar Kaduna, ba karamar nasara ba ce masamman ga daukachin ilahirin al’ummar jihar, ba ma ga al’ummar mazabarsa ba ta Lere, duba da irin hobbasan da yake na samar da ababen more rayuwa ga yankin da yake wakilta a kujerarsa ta Sanatan Kaduna ta tsakiya, tare da samar wa matasa ayyukan dogaro da kai.
Daga nan Hajiya Sharifat ta yi amfani da wannan dama wajen taya kasar nan addu’o’in fatan alheri, tare da addu’ar Allah ya sa a yi zabe lafiya.