A kafa Kwamitin Sasantawa – Domin ci gaban APC a Kano -Usman Dangwari

Zaman ya sa na fito takarar shugabancin Dawanau -In ji Na-mai-tuwo lafiya

Gwamna Abdullahi Ganduje

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Shugaban Kwamitin riko na kungiyar masu sana’ar kayan gwari, Alhaji Usman B. Dan gwari ya ce, idan aka kafa kwamitin sasantawa ko shakka babu jam’iyyar APC za ta sami masalaha da daidaito a jihar Kano da kuma kasa baki daya.

Ya yi tsokacin ne a zantawarsu da manema labarai a Zariya, inda ya jaddada cewa, duk da rikicin cikin gida da jam’iyyar ta APC ke ciki a wadansu jihohin kasar, jam’iyyar tana da karfin da za ta lashe zabbukan shekarar 2023 da za a gudanar nan gaba kadan cikin yardarm Allah.

Dangwari ya kara da cewa, idan jam’iyya tana da magoya baya masu tarin yawa dole ne a sami rigingimun cikin gida tattare da ita, amma idan aka kafa kwamitin sasantawa ko shakka babu kwalliya za ta biya kudin sabulu wajen samun masalaha mai kyau.

Kuma ya bayyana cewa, a shirye suke wajen yin aiki tukuru ta yadda kasar nan za ta ci gaba da samun ci gaba a tsari irin na dimokuradiyya, tare da bunkasa tattalin arziki da kuma samun zaman lafiya mai dorewa tsakanin sassan kasa kamar yadda abubuwa suke tafiya a zamanin baya.

Ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga matasan jihar Kano da kuma na sauran bangarorin kasar nan da su kasance masu bin doka da son zaman lafiya a lokutan yakin neman zabe musamman ganin cewa, sune ake gani a sahun gaba wajen kawo sauyi a shugabanci.

A karshe, Alhaji Usman Dangwari ya yi fatan alheri ga daukacin al’ummar jihar Kano da Nijeriya musamman masu sana’ar gwari wadanda suke a kan gaba wajen samar da ayyukan dogaro da kai da kuma hada kan al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *