A kan Naira 50: Matashi ya yi sanadiyyar mutuwar mai shago

A kan Naira 50: Matashi ya yi sanadiyyar mutuwar mai shago

A kan Naira 50: Matashi ya yi sanadiyyar mutuwar mai shago

Tura wannan Sakon

Daga Zainab Sani Shehu Kiru

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta kama wani matashi mai suna Biodun Adebiyi dan shekara 32, wanda ake zargunsa da laifin dukan wani mai siyar da Taba sigari mai shekaru 30 wanda yayi sanadiyyar cewa ga garinku nan a kan Naira 50.

Ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya fitar ga manema labarai a garin Abeokuta.

Acewar Oyeyemi, an kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da mahaifin marigayin, Adamu Abubaka ya kai shelkwatar Idiroko, inda ya bayyana cewa wanda ake zargin ya zo shagonsa dake unguwar Ajegunle a Idiroko da misalin karfe 2 na rana domin siyan taba sigari tare da dansa, Mukaila Adamu.

Ya ce da misalin karfe 10 na dare wanda ake zargin ya dawo ya bukaci a biya shi N50. Hakan ya haifar da cece-kuce a tsakaninsa da dansa, kuma a cikin ta kaddamar wanda ake zargin ya yi wa dan nasa Mukaila Adamu duka da mari, wanda hakan ya sa dan nasa ya fadi kasa, inda tuni aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Bayan rahoton, DPO yankin reshen Idiroko, CSP Shadrach Oriloye, ya yi gaggawar kai mutanensa wurin da lamarin ya faru, inda nan take aka cafke wanda ake zargin.

Tuni dai aka ajiye gawar marigayin a dakin ajiyar gawarwaki domin gudanar da bincike.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin cikin gaggawa zuwa sashin binciken laifuka da leken asiri na jihar domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da shi a gabam kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *