A Kano: A rage wa makarantu masu zaman kansu kudin haraji -Dokta Sa’idu Mijinyawa

Dalibai a Aji
An yi kira ga gwamnatin jihar Kano ta rage kudin haraji da take karba daga hannun makarantu masu zaman kansu da suke jihar Kano.
Bayanin haka ya fito daga bakin tsohon shugaban kungiyar makarantu masu zaman kansu na jihar Kano, Dokta Sa’idu Mijinyawa, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
Tsohon shugaban kungiyar ya kara da cewa, masu makarantu masu zaman kansu suna bayar da gudunmawa sosai wajen ci gaban harkokin ilimi a jihar tare da samar da aikin yi a cikin al’umma, sannan baya ga samar da kudaden shiga ga gwamnatoci saboda haka yana da kyau ita ma ta rangwanta masu musamman lokacin karbar haraji.
Alhaji Sa’idu Mijinyawa ya yi amfani da wannan dama da kira ga iyayen yara cewa, ya zama wajibi su kula tare da bayar da muhimmanci a kan ilimin yaransu tare da ba su tarbiya, sannan yana da kyau su rika kai ziyara makarantu domin sanin halin da ilimi yake ciki.
Daga karshe, ya ce, lokaci ya yi da al’umma za su hadu domin taimaka wa harkokin ilimi, gwamnati ita kadai ba za ta iya ba dole sai an hadu.