A Kano: ADC ta bai wa Khalil takara

A Kano: ADC ta bai wa Khalil takara

Sheikh Khalil Dantakara ADC

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Fitaccen malamin addinin Misulincin nan, Malam Ibrahim Khalil ya zama dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar ADC, babu hamayya.

Malam Ibrahim Khalil, wanda ya sami takarar a yayin taron kaddamar da takarar tasa da kuma mika masa fom takarar, wanda aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata, a gidan Mambayya, Unguwar Gwammaja cikin birnin Kano.

A lokacin da yake mika masa fom, shugaban jamiyyar na kasa, Cif Ralph Okey Nwosu ya bayyana cewa, an tabbatar da Malam Ibrahim Khalil a matsayin dan takarar gwamnan Kano a karkashin jam’iyyar ADC a zaben gwamna na shekara mai zuwa saboda gaskiyarsa da kuma cancantarsa Shugaban jam’iyyar wanda ya bayyana kyawawan akidun jam’iyyar ADC, ya kuma karfafa cewa, Malam Ibrahim Khalil shi ne kadai dan takarar da zai tsamo jihar Kano daga halin da take ciki.

Ya kuma tabbatar da kudurin jam’iyyarsu na bai wa mata kaso 35 cikin 100 na mukamai da kuma kudirin jam’iyyar na taimaka wa matasa su cim ma burinsu na rayuwa.

Da yake bayyana takaicinsa bisa abin da ya kira bata arzikin kasa da kuma dora abubuwa a inda ba su dace ba da manyan jam’iyyun APC da PDP suka yi a kasa, Cif Ralph ya hori ‘yan Nijeriya da su yi watsi da wadannan jam’iyyun, inda ya ce, jam’iyyun ba su kai kasar tafarkin ci gaba ba.

Da yake jawabi bayan ya karbi fom, dan takarar gwamnan, Malam Ibrahim Khalil, ya yi alkawarin adalci da kuma bin doka da oda wadanda za su zame masa linzami a mulkinsa, idan har ya sami nasarar zama gwamnan Kano.

Malam Ibrahim Khalil, tsohon dan takarar gwamna ne a jam’iyyar PDP, kafin daga bisani ya koma jam’iyyar APC, sai kuma a halin yanzu da yake a jam’iyyar ADC, ya yi alkawarin bai wa harkar ilimi muhimmanci da lafiya da ci gaban matasa da kuma bunkasa tattalin arziki, inda ya roki mutanen Kano da su zabe shi domin kawo ci gaba mai dorewa a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *