A Kano: An karama fittatun jami’an tsaro -Saboda kwazo

A Kano: An karama fittatun jami’an tsaro -Saboda kwazo

An karama fittatun jami’an tsaro

Tura wannan Sakon

Daga Rabiu Sunusi

A ranar Lahadin da ta gabata kungiyar ci gaban al’ummar jihar Kano ta karrama wadansu daga cikin zakakuren jami’an tsaro da suke aiki tukuru a wadansu sassa na cikin birnin Kano.

Taron ya gudana a Tal’udu karamar hukumar Gwale da ke cikin birnin Kano karkashin jagorancin shugaban kungiyar ci gaban al’ummar jihar Kano, Malam Abdurrazak Salisu Ibrahim da sauran mukarrabansa.

Da yake jawabinsa shugaban kungiyar, Abdurrazak Salisu Ibrahim ya bayyana cewa, lallai irin gudunmuwar da jami’an tsaro suke bayar wa a jihar Kano da unguwannin, shi ne ya ja hankalisu da babu abin da ya kamata su yi wajen sakama masu face karrama su.

Shugaban ya kara da cewa, idan aka dauki misalin Kwamishinan ‘yan-sandan jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya dora jami’an sa kan hanyar da ta dace kan aiki tukuru ba tare da karbar rashawa ba ballantana ma cin hanci.

Sannan Abdurrazak ya tabbatar da cewa, zuwan Bashir Musa Gwadabe ya timaka wa yankinsu gaya matuka wajen kakkabe ‘yan daba da masu shaye-shaye a cikin unguwanninsu, da ma jihar Kano baki daya.

Shugaban ya tabbatar da cewa, lallai babu makawa suna jinjina wa wadannan jami’an tsaro bisa jajircewarsu na kauda fadan daba da kwacen waya a cikin garin Kano, hakazalika kamar DPO na Mandawari, Baba Ali shi ma yana aiki tukuru.

Bayan wadannan jami’an akwai kakakin yada labaran ‘yan-sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya jajirce wajen tabbatar dukkan ayyukansa sun tabbata kan hayar da aka dora shi. Shi ma da yake nasa jawabin lokacin taron bisa namijn kokarin wadannan matasa, kwamishinan ya kora da cewa, lallai tun da yake aiki a jihohi daban-daban a kasar nan bai ga inda ake nuna wa jami’an tsaro soyayya ba irin jihar Kano. Sannan kuma yaba bisa yadda al’ummar jihar suke taimaka wa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu a cikinsu.

Daga na ya nuna godoyar sa ga gwamnati jihar Kano bisa hadin kan da suke ba su wajen gudanar da aikinsu matsayinsu na jami’an tsaro, hakazalika kuma kara mika godiyarsu ga dukkann wadanda suke ba su goyon baya wajen gudanar da aikinsu a fadin jihar Kano.

Daga karshe, ya yi kira ga ga iyayen yara wajen kula da ‘ya’yansu bisa yadda ake samun kananan yara wajen aikata laifuffuka daban-daban a jihar Kano, domin haka ne ya yi alkawarin ci gaba da yi wa al’ummar jihar Kano aiki bisa gaskiya da rikon amana kamar yadda ya yi alkawari tun farko.

Cikin wadanda aka karrama sun hada da kwamishinan ‘yan-sandan jihar Kano, CP Sama’ila Suha’aibu Dikko da SP Abdullahi Haruna Kiyawa da CSP Bashir Musa Gwadabe da shugaban Karota, Baffa Danagundi da DCP Balarabe Sule da DOP Mandawari Baba Ali da SP Shehu Dahiru, OC anti kidnapping sai SP Bello Yakubu tare da SP Nasiru Haruna da dai sauran su.

Taron ya samu halartar manyan Yankasuwa da ma’aikatan gwamnati da masu unguwanni da sauran masu ruwa da tsaki na jahar kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *