A kano: An yi gangamin nuna goyon baya ga takatar Osibanjo

a kano: An yi gangamin nuna goyon baya ga takatar Osibanjo

Gangamin nuna goyon baya ga takatar Osibanjo

Tura wannan Sakon

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Wadansu gamayyar kungiyoyi masu kira da goyon bayan mataimakin shugaban kasa Farfesa Yomi.Osibanjo da ya fito takarar neman shugabancin kasa a shekarar 2023 karkashin jagorancin Honarabul Sagir Wada Mai-Iyali sun gudanar da gangami domin nuna farin ciki bisa amsa kira da mataimakin shugaban kasa ya yi na ayyana amincewarsa.

Taron gangamin wanda aka gudanar a harabar ofishin gamayyar kungiyoyin ya sami halartar dinbin jama’a da suka hada da wasu jiga-jigan APC da suka hada da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar da Honarabul Aliko Sha’aibu, tsohon dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Birnin Kano da sauran mutane maza da mata daga kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

Da yake jawabi yayin gangamin, shugaban kungiyar Osibanjo Solidarity Groups na kasa, Honarabul Sagir Wada Mai-Iyali ya ce, sun shirya taron ne domin nuna farin ciki da yadda mataimakin shugaban kasa ya amsa kiraye-kirayen da suke masa duba da cewa irinsu ake bukata a kasar nan. Ya kara da cewa, Osibanjo mutum ne da ba shi da kabilanci da nuna banbancin yare ko addini, abin da yake da bukata shi ne ci gaban ‘yan kasa da yin aiki tukuru a tafiyarsa da Buhari.

Ya ce, mataimakin shugaban zai zo ne kawai ya dora a kan ayyukan da suka somo na ci gaba saboda da ma ya san komai don haka suke fatan alkhairi a gare shi idan Allah ya ba shi wannan kujera ta shugaban kasa, za a sami dorewar ci gaba. Mai-Iyali ya ce, wannan tattaki na gangami shi ne mataki na farko bayan amsa kiransu, inda ya kara da cewa, sun dade suna yawatawa sassan kasar nan domin rokonsa a kan ya tsaya kuma Allah ya yarda ya amince ya tsaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *