A Kano: Buhari zai kaddamar da ayyukan raya kasa

Tura wannan Sakon

…. Ciki har da hasken lantarki

A ranar Talata 30 ga Janairu, 2023, gwamnan Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai karbi bakuncin shugaban kasa kuma babban kwamandan askarawan Nijeriya, Muhammadu Buhari.

Sanarwar da ta fito daga ofishin kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ta ce, ziyarar ta kwana biyu za ta bai wa shugaba Buhari damar kaddamar da ayyukan raya kasa birjik.

Da farko shugaban zai kaddamar da tashar hasken lantarki mallakar jihar ta farko mai karfin megawat 10 da katafariyar gadar nan ta Hotoro wacce aka lakaba wa suna gadar Muhammadu Buhari.

Sauran sun hada da cibiyar kiwon lafiya ta cutar daji wadda aka gina a kan biliyoyin Naira da rukunin gidajen malamai 700 da cibiyar koyon sana’o’in hannu iri-iri mai suna Dangote da tashar tsandauri da ke Zawaciki da kuma tashoshin samar da hasken rana da kananan masana’antu da tashar tace ruwa Tamburawa da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *