A Kano: Farashin kayayyakin abinci ya sauka -In ji Dan Ibadan

Tura wannan Sakon

Labari daga Musa Diso

Kakakin kungiyar masu sayar da hatsi da ke kasuwar Dawanau, Abubakar Ibrahim Dan Ibadan ya ce, saboda mahimmancin wannan wata na Ramadan kungiyar kasuwar Dawanau ta samar da rangwamen farashin kayan abinci domin samun falalar watan.

Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin Albishir a birnin Kano a makon da ya gabata, ya ce, hakika watan yana da mahimmanci ga al’ummar Musulmi don haka a jajirce da kuma kokarin ganin jama’a sun sami falalar wannan wata mai albarka.

Dan Ibadan ya yi kira ga sauran ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi da su yi koyi da kasuwar hatsi ta Dawanau domin saukaka wa al’umma da kuma neman yardar Ubangiji.

Ya kara da cewa, tallafawa da mawadata suke yi ga matalauta a wannan wata mai albarka shi ke kawo soyayya da kauna a tsakanin al’umma, don haka wannan wata wata dama ce ga al’ummar Musulmi masu son kyakkyawan sakamako da makoma mai kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *