A Kano: Fiye da mutane dubu 36 ke sana’ar tifa -Kwamred Mamuni Takai

Kwamred Mamu

Kwamred Mamuni Takai

Tura wannan Sakon

Fiye mutane dubu 36 suke cin abin a bangaren sana’a ta aikin tifa a fadin jihar Kano.

Hakan na fitowa ne daga bakin shugaban hadaddiyar kungiyar direbobin tifa na kasa reshen jihar Kano, Kwamred Mamu Ibrahim Takai a wata zantawa da wakilin Albishir makon jiya.

Kwamred Mamu ya kuma tabbatar da cewa, lallai tafiyar ta su ta yi nasara daban-daban a zuwansa sabanin da a baya. Wadansu daga cikin ayyukan da suka samu karkashin kulawarsa sun hada da samar da katafariyar sakatariyar da ba kowace kungiya a jihar Kano ba.

Shugaban ya kuma tabbatar da bude kofa ne ga dukkan membobin kungiyar tare da iyayen kungiya da ba su dama domin shigowa tare da bayar da dukkan shawarwari da tsawatarwa.

Sannan kuma ya ce, ga aikin su ne wajen kare hakkin dan kungiya tare da kare hakkin al’umma d asuke tare da su. Mamu ya kuma tabbatar da cewa, sun gudanar da taron bitoci ga ‘ya’yan kungiya ta yadda za su mayar da hankali wajen aikinsu.

Sannan ya kuma cewa, sun kuma tallafa wa ya’yan ‘yan kungiya musamman wadanda iyayensu suka mutu suka bar su, kazalika sun kuma kawo tsarin mayar da ‘ya’yan kungiya wajen karatu.

Bayan karatun zamani sun kuma taimaka wa yara kan karatun addini, sannan ya kuma kara da cewa, suna sama masu mafita da madogara domin cim ma nasara.

Hakazalika ya ce, sanda suka zo wannan kujera ba su samu Naira daya ba amma kuma yanzu sun sama wa kungiya fili na ta na kanta tare da gina katafariyar sakatariyar.

Sai batun gyara hanyoyin da suke bi wajen aikinsu inda suka samun hadin kan al’ummar yankunan da suke gudanar da aikinsu. Takai ya ce, kuma suna kokarin ganin sun gina asibitinsu na kansu, tare da bayar da tallafin tifofin kasa da yashi ga bangarori da dama.

Sannan ya kuma jahankalin matasa wajen raina karamar sana’a musamman ta aikin tifa wannan ba daidai ba ne, domin kuwa shi da ya fara sana’ar mota ya fara ne daga yaran mota ya zama direba ya kuma kama aikin gwamnati wanda daga bisani ya yi sana’ar saida tabarmar leda ya kuma yi aikin gwamnati tare da da komawa kan aikin mota.

Ya kuma ce, matsalolin da kungiyar take fuskanta a baya yanzu cikin yardar Allah sun kau, ya kuma bukaci jama’a da su tunatar da su idan sun ga kuskure a harkarsu.

Mamu ya kuma bukaci gwamnati da ta sa su cikin tsarin kwangiloli idan hakan ya bijiro domin taimaka wa ma’aikatansu, sannan ya kuma ce yana da kyau gwamnati ta saya wa membobinta motoci. Ya kuma roki gwamnati da ta taimaka wajen samar da tashoshin da ya kamata ‘yan tifa su rinka ajiye motocinsu domin samun haraji.

Ya kuma ya ba ga yadda ‘yan kungiya wajen yadda suke biyayya tare da kara hada kai, ya kuma nuna godiyar su ga al’umma jihar Kano wajen gudunmuwar da suke ba su wajen aikinsu ya kuma ce insha Allahu ba za su ba su kunya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *