A Kano: FOMWAN ta tallafa wa marayu 100 da kayan abinci

FOMWAN ta tallafa wa marayu 100 da kayan abinci
Daga Alhussain Kano
Kungiyar mata Musulmi ta FOMWAN rehen jihar Kano a karkashin shugabancin Malama Binta Abubakar Muhammad, ta tallafawa wadansu daga cikin marayun jihar Kano kimanin 100 da kayan abinci, wanda wata kungiya mai suna Darul- Arkan daga kasar Masar ta samar da abinci aka kuma rarraba ta hannun FOMWAN.
Da take jawabi ga manema labarai, Amirar FOMWAN ta ce, abincin sun hada da Shinkafa da Taliya da sauran abinci kala daban-daban.
A jawabinta, Malam Binta ta ce, marayun sun nuna matukar farin cikin su da murna da tallafin da suka samu sai ta hore su da su amfani da kayan abincin ta hanyar da suka kamata musamman ganin halin da ake ciki na matsin rayuwa . Hajiya Binta Abubakar Muhammad wanda har ila yau ma’aikaciya ce a hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta yi kira ga masu hali da kuma kungiyoyi da su rika taimaka wa marasa galihu musamman marayu da marasa gata.
Daga karshe, ta jinjina wa Gidauniyar Darul-Arkam a kan tunanin da ta yin a tallafa wa marayun kyauta aka rarraba ta hannun kungiyar FOMWAN wannan karrama wa da aka yi masu sun ji dadi sosai.