A Kano: Gwamna ya fara nadin sababbin mukamai

Tura wannan Sakon

Daga Rabi’u Sanusi Kano

Sabon gwamnan jihar Kano da ya karbi rantsuwar kama aiki a ranar Litinin, ya fara gabatar da nadin mukamai na mataimakan da za su taimaka masa a gwamnatinsa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara nadin da sakataren gwamnati jiha da Dokta Baffa Bichi ya zama sabon sakataren gwamnati jihar Kano, sai Shehu Wada Sagagi a matsayin shugaban ma’aikata.

Sauran mukaman sun hadar da Dokta Farouk Kurawa a matsayin PPS, sai Abdullahi Ibrahim Rogo da ke da mukamin shugaban tsare-tsare watau, yayin da Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa yake matsayin Sakataren yada labaran gwamnan a yanzu.

Bayanin na dauke a wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan na jihar Kano, Malam Sanusi Bature ya fitar ga manena labarai a daren ranar Litinin dauke da sa hannunsa.

Kazalika sanarwar ta ce, dukkan wadanda aka bai wa mukaman sun kasance a matakin cancanta da kwarewa tare da irin gudunmuwar da suke bayar wa wajen ganin jihar Kano ta ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *