A Kano : Gwamnati ta amince da daukar ma’aikatan lafiya sama da 500

A Kano Gwamnati ta amince da daukar ma’aikatan lafiya sama da 500

A Kano Gwamnati ta amince da daukar ma’aikatan lafiya sama da 500

Tura wannan Sakon

Daga Usman Usman Garba

A kudurinsa na kai bangaren kiwon lafiya zuwa babban matsayi, gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da a dauki sababbin ma’aikatan kiwon lafiya sama da 500, wadanda suka hada da Likitoci, da masana hada magunguna da kuma masu Kimiyyar binkicen kwayoyin cuta, da sauran kwararrun masana kiwon lafiya.

Kwamishinan lafiya na jihar ,Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan a lokacin da gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje take raba takardun sheda ga daliban da suka kammala karatunsu a jami’o’in da suke Sudan, wanda aka gudanar a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin jihar.

Tsanyawa ya ci gaba da cewa, “A kokarinsa ci gaban bangaren lafiya, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umurce mu da mu zagaya zuwa daukacin cibiyoyin lafiya 484 dake jihar domin sanin halin da suke ciki”

Dokta Tsanyawa ya bayyana cewa, gwamna Ganduje ya kuma sake bayar da izinin daukar wasu karin ma’aikatan kula da lafiya 1,500, wadanda za a tura su zuwa wadannan cibiyoyin kiwon lafiya 484.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *