A Kano: Gwamnati ta yi alkawarin kulawa da marayu

A Kano: Gwamnati ta yi alkawarin kulawa da marayu

A Kano: Gwamnati ta yi alkawarin kulawa da marayu

Tura wannan Sakon

Daga Muhammad Mustapha Abdullahi

Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje, (Khadimul Islam), ta yi alkawarin ci gaba da kulawa da marayu da ke fadin jihar nan.

Gwamnan ya bayyana hakan, a dakin taro na Afirka House, yayin da ake gabatar da shan ruwa tare da marayu, inda ya ce, ya zamar masu dole da su ci gaba da kulawa da marayu, kamar yadda Allah da Manzonsa suka kwadaitar da yin hakan. Ganduje ya kara da yin godiya ga dukkanin mutanen jihar Kano da suke kulawa da irin wadannan marayu, tare da wadanda suke zuwa har gidajen marayun domin su duba su, su ba su tallafi. Ya kara da cewa, sun shirya wannan shan ruwa na musamman da marayu, ba don su ba su abin da za su ci ba, ko su sha, sai don su ji dadi, su ga kamar iyayensu suna nan.

A na ta bangaren kwamishiniyar mata ta jihar Kano, Hajiya Zahra’u Muhammad Umar, cewa ta yi, gwamnatin jihar Kano na ba da tallafi, da goyon baya ta kowane fanni, da ya shafi marayu sama da 470, da ya hada da lafiyarsu. Ta kara yin godiya ga gwamnati bisa yadda ta ke ba da goyon baya, inda ta ce, ta na tabbatar wa da mai girma gwamnan jihar Kano, suna da abincin da za su ciyar da marayu har na tsawon shkara daya, ba tare da wata matsala ba.

Sannan ina kara sanar da mai girma gwamna cewa, marayu a jihar nan, a sa su a tsarin lafiya na inshore, kamar yadda ma’aikatan jihar suke. A karshe, ina kara sanar da mai girma gwamna cewa, ‘marayu a jihar Kano, kullum a cikin yi maka addu’a kai da gwamnati su ke, sakamakon yadda ka ke dawainiya tare da kulawa da s, ba tare da nuna gajiyawa ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *