A Kano: Gwamnati za ta taimaka wa Jam’iyyar Matan Arewa

Tura wannan Sakon

Gwamnati za ta taimaka wa Jam’iyyar Matan Arewa

Tura wannan Sakon

Daga Alhussain Kano

Gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, za ta taimaka wa jam’iyyar matan Arewa ta jihar Kano, da kayan sana’oin dogaro da kai da sauransu, kamar yadda shugabanta ta jihar, Hajiya Ummi Tanko Yakasai ta shaidawa manema labarai kwanakin baya.

Malama Ummi Tanko Yakasai ta ce, babu shakka idan mata suka samu tallafin zai taimaka masu sosai wajen tafiyar da harkokinsu musamman matan da mazajensu suka rasu. Shugabar ta gode wa gwamnan a kan aniyarsa ta alhairi ga jam’iyyar.

Hajiya Ummi Tanko ta gode wa ‘yan-kungiyar da ke fadin jihar Kano, a kan yadda suke ba ta hadin kai da goyon baya wajen tafiyar da shugancinta, wani abin alfahiri shi ne, yadda ake kara samun mata na shigowa jam’iyyar matan Arewa akaiakai wannan nasara ce babba wanda ita da ‘yan-kungiyar ba za su manta da shi ba.

Ummi ta nuna damuwarta a kan yadda yankin Arewacin kasar nan ya shiga na matsalar tsaro wanda wani lokaci kan shafar mata da kananan yara musamman a shekarar 2021duk da gwamnati na bakin kokarin ta a kan tsaron, ya kamata ta rubanya a shekarar 2022, amma su ma al’umma ya kamata su taimaka wa gwamnati a kan tsaro sannan a koma ga Allah tare da yawaita addu’a dare da rana idan aka dage a kan haka za’a samu nasara da yardar Allah.

Zaben 2023 da ke tafe ta yi kira ga iyayen yara cewa, ya zama wajibi su kara sanya idanu a kan tarbiyarsu su sani Allah zai tambaye su ranar gobi kiyama. Daga karshe, ta kawo shawarar cewa, al’umma su rinka kafa kwamitocin da za su rinka kula tare da sanya idanu a kan zirga-zirgar al’umma, wannan zai taimaka sosai ta fannini tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *