A Kano: Hana A-Daidaita hawa tituna, rage hadari -Baffa Dan-agundi

Baffa Dan Agundi
Daga Rabi’u Sanusi Kano
Shugaban hukumar kula da ababen hawa da sufuri ta jihar Kano, Baffa Babba Dan Agundi ya bayyana cewa, matakin da gwamnatin Kano ta dauka na hana ‘yan Adaidaita Sahu hawa titunan Hadeja da Gwarzo ba shi da nasaba da hana su hanyar dogaro da kai.
Baffa,ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudana a ofishinsa ranar Larabar da ta gabata domin magance tsegunguma da wadansu suke yi na gabatar da dokar da ke da alaka da rage samun hadari kan titunan da ke yawan faruwa. Shugaban Karota ya bayyana titun Hadeja Road dokar za ta fara daga shataletalen Mudubawa zuwa Gezawa ne dokar zatai aiki a kansa, sai daga shataletalen Tal’udu zuwa Gwarzo shi ma ba a amince wa masu baburan Adaidata Sahun ba.
Haka kuma ya yi maganar masu tsallaka tituna misalin daga Badawa zuwa Dakata ko daga Dakata zuwa Badawa dokar ba za ta yi aiki a kansu ba. “A nan zan yi amfani da wannan dama domin mika godiyarmu ga masu baburan Adaidata Sahu da suke daukar kaya a kasuwar ‘Yankaba saboda kokarin bin dokoki da suke yi.”
Kazalika ya bayyana bukatar da ke akwai na hana sauran manyan titunan da ke mahada na shigowa cikin garin ko fita da ciki da zarar gwamnati ta samar da motocin da za su ci gaba safarar al’umma kan titunan.
Daga bangaren shugaban kungiyar masu baburan Adaidata Sahu na jihar Kano, Alhaji Mansur Tanimu yayin da wakilinmu ya tuntube su kan batun.
Ya ce, lallai suna da masaniya kan wannan doka, amma kuma su ma ba sauran membobinsu da su kwantar da hankalinsu. Ya kara da batun cewa, matsayinsu na shugabanni suna kokarin zama da gwamnati domin duba al’amuran da ya dace kasancewar batun ya zo masu babu tsammani.
Su ma wadansu masu hawa sun nuna matukar damuwarsu ta yadda suke cewa, hakan zai iya kawo masu tasgaro a gudanar da harkokinsu na yau da kullum, yayin da wadansu suke cewa, ba lallai ba ne motoci su iya shiga cikin lunguna da isar da su inda ya kamata su isa ba.