A Kano: Hantarar likitoci ga majiyyata ta kai kololuwa

Daga Zainab Sani Shehu Kiru
Matsalar nan ta kyara da ma hantara gami da nuna halin ko-inkula da wadansu likitoci ke yi wa marasa lafiya, wanda hakan ke haifar da jikkatar marasa lafiyar Hakan ne ya sa wadansu kan yin shakkar zuwa asibitocin da gwamnati ta samar wa al’ummarta domin guje wa wulakanta da ma jigata kafin a duba su, sukan yi kokari su tafi asibitoci masu zaman kansu domin a duba lafiyarsu.
Wani babban asibiti wanda ya shahara a cikin birnin nan kuma ya hada da kwararrun likitoci wadanda wadansu daga cikinsu kan yi biris da marasa lafiyar, a cewarsu ba su da wajen ajiye su ko da kuwa marar lafiyar nan na matukar bukatar kulawarsu ta gaggawa.
Mata masu haihuwa su ma ba su tsira ba daga wannan halin ko-in-kula, su ma masu shara da goge-goge su ma ba a bar su a baya ba wajen kyarar marasa lafiya.
Duk da kasancewar ba su suke da hakkin duba masu haihuwar ba iyakarsu idan an haihu su gyara wajen da aka yi haihuwar, wadansu majiyyata da ma masu jiyyarsu kan yi tir da halayen da ake nuna masu a asibitocin gwamnati