A Kano: Hukumar kashe gobara ta sami motar kashe gobara

A Kano: Hukumar kashe gobara ta sami motar kashe gobara

A A Zaura Foundation

Tura wannan Sakon

Daga Muhammad Mustapha Abdullahi

A ci gaba da kokarin inganta lafiya da tsaro da dukiyar al’umma, gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta bai wa hukumar kashe gobara ta jihar Kano motar kashe gobara da ta agaji.

Karkashin jagorancin gwamna ta bayar da tallafin ne ta ofishin kwamishinan ayyuka, Injiniya Idris Wada Saleh, wanda gwamnatin ta sa mu tallafin ne daga Gidauniyar Alhaji Abdulkarim A A Zaura domin tallafa wa gwamnati jihar Kano wajen ci ayyukan kare rayuwa da dukiyoyin al’umma wanda annobar gobara ta ke haifar wa a jihar Kano.

A na sa bangaren, Daraktan hukumar kashe gobara a jihar Kano, Alhaji Hassan Ahmad Muhammad kira ya yi ga sauran jama’a masu hannu da shuni da sauran kungiyoyi masu burin taimaka wa al’umma da su yi koyi da abin da Abdulkarim A.A Zaura ya ke na taimakon al’umma a jihar Kano.

A wani labarin kuma, mai magana da yawunta SFS Saminu Yusif Abdullahi ya ce, sun karbi kira daga ofishin da ke karamar hukumar Kura da misalin karfe 7 ta bakin jami’in hukumar ‘yan sanda mai suna Sargent Zarewa, inda ya sanar da mu aukuwar hatsarin hanya tare da tashin gobara a kan titin Zariya.

Saminu Yusuf ya kara da cewa, dukkanin wanda hatsarin ya rutsa da su an samu nasarar ceton su a raye ba tare da rasa ransa ba, wanda an dauke su zuwa asibitin kwararru na Kura domin duba lafiyarsu da ba su agajin gaggawa inda suka sami raunuka, musabbabin faruwa hatsarin shi ne, gudun wuce sa’a da kuma yunkurin wuce motar da ba’a samu damar yin hakan ba, wanda a karshe muna amfani da wannan da ma wajen kira ga direbobi da su rinka bin ka’idoji da dokokin hanya domin kare lafiya da dukiyoyinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *