A Kano: Hukumar kashe gobara ta shirya fadakar da al’umma

Daga Wakilinmu
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, a karkashin jagorancin Alhaji Hassan Ahmad Muhammad, ta kammala shirye shiryen da suka kamata, wajen fadakarwa tare da wayar da kan al’ummar jihar, musamman a wannan lokaci da ake ciki na hunturu da kuma iska, domin kaucewa aukuwar tashin gobara a gidaje da kasuwanni da sauransu.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin mai kula da shashin ma’aikatar, Alhaji Jamilu Bashir (HFS) a wata takarda da ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai. Alhaji Jamilu Bashir, ya kara da cewa, duk shekara irin wannan lokacin a kan fadakar da al’ummar jihar.
Tashoshin dake kwaryar birnin Kano sha biyar suma za su kaddamar da na su shirin wayar da kan a tashoshin kashe gobara sha biyu. Tashar kashe gobara dake garin Bichi, ita za ta kula da yankin masarautar dake masautan ta haka tashar dake garin Gaya da sauran su .
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano za ta sanaya idanu sosai aduk inda za’a gunar da aikin fadakarwa domin dai ganin shirin ya zamu nasaran da ake bukata da yardarm Allah inji Jamilu Bashir [HFS] FAIRE Prevention Officer.