A Kano: JIBWIS ta kaddamar da bangaren Nisa’us-Sunnah, masarautar Rano

JIBWIS ta kaddamar da bangaren Nisa’us-Sunnah
Daga Mahmud Gambo Sani
A ranar Asabar da ta gabata, Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatil-sunnah, reshen jihar Kano, ta kaddamar da bangaren mata (Nisa’ussunnah) na masarautar Rano, a garin Tudun Wadar Dankadai.
Da yake gabatar da jawabi ta hannun sakataren jiha, Mallam Hassan Binyamin Mandawari, shugabanta na jiha, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya yi bayani daki-daki kan muhimmancin da mata ke da shi wajen gina tarbiyyar addinin Musulinci.
Ya ce, kasancewar mata ginshikin tarbiyya ga al’umma, ya wajaba su ja ragamar daukaka addini daga tushe tamkar yadda matan sahabbai da tabi’ai suka yi a zamaninsu.
Farfesa Pakistan ya yi magana kan mace tagari da siffofinta wadanda suka hada da; a duk lokacin da maigida ya dub eta takan faranta masa rai, idan kuma da ya gida, za ta kare masa mutuncinta, kamar yadda hakan ya tabbata daga Annabin rahama.
Har ila yau ya ce, mace tagari takan karfafa mijinta a kan neman halal da kawar da shi daga fadawa cikin haram. Daga nan sai ya lissafa gudummowar matan da suka gabata, wadanda suka hada da matan sahabbai da na tabi’ai har zuwa zamanin Shehu Usmanu Danfodiyo, inda aka sami ’yar Shehun Nana Asma’u ta yi shuhura a kan nema da yada ilimi.
A nata jawabin, Amira ta jihar Kano, Zainab Ja’afar Mahmud Adam, ta yi tsokaci kan bukatar da ke akwai ta mata su nemi ilimi gadangadan tare da amfani da ilimin wajen dabbaka Sannah da yayata ta lungu da sako.
A karshe, mai masaukin baki kuma shugabar Nisa’ussunnah a karamar hukumar Tudun Wada, Hajiya Lubabatu Sani, ta gode wa shugabannin JIBWIS na jiha bisa jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, wanda ya sami wakilcin sakataren jiha, Mallam Hassan Binyamin Mandawari da Amira Zainah Ja’afar Mahmud Adam da kuma ilahirin wadanda suka sami zarafin halartar kaddamar da shiyyar Rano ta Nisa’ussunnah.