A Kano: Jirgin kasa ya yi taho mu gama da tankar siminti

Daga Muhammad Mustapha Abdullahi
A ci gaba da kokarinta na kare rayuwa da dukiyoyin al’umma hukumar kashe gobara ta jihar Kano karkashin jagorancin Darakta Alhaji Hassan Ahmad Muhammad, ta bakin mai magana da yawun hukumar, SFS Saminu Yusuf Abdullahi sun sami kira ta bakin Musa Bello inda ya sanar da mu aukuwar hatsari tsakanin jirgin kasa mai dauke da fasinja da ya taho daga Legas da motar siminti ta Dangote a kan titin Obasanjo da ke cikin birnin Kano.
Saminu Yusuf ya ce, da samun labarin aukuwar lamarin, muka tura jami’an mu domin bayar da taimakon gaggawa, inda muka iske jirgin kasa ne da ya taso daga Ikko ya doki motar siminti ta Dangote da baburin A daidaita Sahu mai lamba 2153 TRN, inda jami’anmu suka samu nasarar ceton mutane 6 a raye, wanda 4 daga cikinsu su ne a cikin A daidaita Sahun, sai mutane biyu da suke zaune kusa da wani masallaci da ya ke kusa da inda lamarin ya faru.
Saminu Yusuf ya ce, sun dauki mutanen da lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke birnin Kano, inda bayan dubawar jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwar Abdulwahabu dan shekara shekaru 32, wanda shi ne matukin A Daidaita Sahun, sannan muka mika shi zuwa wajen jami’ar ‘yan-sanda Aisha Alasan domin mikashi ga ‘yan’wansa.
A karshe muna amfani da wannan da ma wajen kara kira da jan hankali ga al’umma da su rinka bin ka’idojin da hukumar kashe gobara ta shimfida domin kaucewar aukuwar hadarin gobara da hadarin hanya