A Kano: Kashi 16 cikin 100 na ta’ammali da kwaya –Marwa

yan kwaya

Tura wannan Sakon

Shugaban Hukumar Hana Ta’ammuli da Kwayoyi ta Nijeriya, Buba Marwa ya ce, akalla kashi 16 na al’ummar jihar Kano ‘yan kwaya ne, watau kwatankwacin mutane miliyan biyu kenan.

Marwa ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da ya kai wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

A jihar Kano, ta’ammuli da kwayoyi na da kashi 16, ma’ana a cikin mutane shida, mutun daya dan kwaya ne, kuma shekarunsu na tsakan-kanin 15 zuwa 64”.

In ji Marwa. Shugaban NDLEA ya kara da cewa, jihar Kano na da kusan mutane miliyan 2 da ke kwankwadar kwayar Tramadol da Codeine da sauran magungunan maye, amma ban da wiwi.

Marwa ya roki gwamnatin Kano da ta kafa wata doka da za ta hana ‘yan siyasa bai wa matasa kwayoyi. Kazalika ya bukaci gwamnati da ta tilasta wa jama’a yin gwajin kwayoyi gabanin daurin aure, matakin da ya ce, zai taka rawa wajen magance matsalar tsakanin al’umma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *