A Kano: Kotu ta dakatar da zaman tuhumar Abdul-Jabbar

Tura wannan Sakon

Kotun Majistare mai lamba 12,a karkashin babban mai shari’a, Muhammad ta dakatar da zaman tuhumar da Malamai za su yi wa Mal. Abdul-Jabbar tare da bayar da umarni kan hukuncin kotu na farko da ta yanke ranar 8 ga Fabrairu,2021 na hana Abdul-Jabbar gudanar da wa’azi da karantarwa a jihar.

Idan za a iya tunawa,tuni shugaban Majalisar Makaman Kano kuma mukaddashinta na kasa. Sheikh Ibrahim Khalil ya bayar da haske kan cewa,zaman tuhuma za a yi da malamin ba Mukabala ba,kamar yadda gama-garin mutane ke gani ko suke fada.

Babbar kotun,a hukuncinta na farko ta haramta wa dukkan kafaren yada labarai, wala’alla rediyo ko telebijin ko jarida ko mujalla,yayata koyarwar malamin wadanda suka kunshi yi wa addini ta’annati da baragada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *