A Kano: Kungiyar mazan-jiya ta bayyana goyon baya ga gwamnati

Hadaddiyar kungiyar tsofaffin sojoji ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin jihar Kano a dukkanin ayyukanta na ci gaban al’umma da kasa baki daya.
Sakataren kungiyar na jihar Kano, Sani Abdul ya bayyana hakan ga manema labarai a makun jiya.
Ya bayyana cewa, kungiyar tana tafiyar da ayyukanta kamar yadda ya kamata, kuma tana biyayya ga uwar kungiyar ta kasa.
Ya ce, hakika ayyukan kungiyar shi ne kula da jin dadin dukkanin tsofaffin sojojin da suka shiga kungiyar bayan sun kammala aikinsu.
Ya jaddada bayyana goyon bayan shugabanni kungiyar ga gwamnati bisa la’akari da yadda take tallafa masu ta hanyoyin da suka kamata, A hannun guda kuwa ya bayyana rashin gamsuwarsa bisa rashin bayar da gudunmawa daga masu hannu da shuni domin tallafa wa ‘yan kungiyar domin tafiyar da harkokin iyalan ‘yan kungiyar domin samar masu ingantacciyar lafiya da ilimi da taimaka wa wajen aurar da ‘ya’yansu mata.
Haka kuma ya kara bayyana babbar matsalar da tsofaffin sojoji ke fuskanta bisa rashin biyansu hakkokinsu a wuraren da aka daukesu aikin gadi na dai-daikun jama’aya bayyana cewa, farin ciki da kuma tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihim Wassallam ne ya sa ya shirya taron, domin bayyana darajoji da karamomi na fiyayyen halitta.
Ya kara da cewa, nuna wa al’umma irin halayen Annabi Muhammad Sallallahu Alaihim Wassallam da kuma koyi da su musamman ga matasa da yara manyan gobe shi ne makasudin gabatar da taron Maulidin.
An gudanar da Maulidin a karkashin jagorancin zawiyyar Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Sheikh Muddasir ya yi alkawarin ci gaba da shirya tarurrukan Maulidin duk shekara.
Shehunan Malamai daga sassan Kano da kewaye suka gabatar da makalu a kan tarihin rayuwar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihim Wassallam, yayin da daliban ilimi suka gabatar da wakokin nuna soyayyarsu ga Annabi Muhammad SAW. Malamai da Kadimai da Madihai da ‘yan-kasuwa da jami’an tsaro suka halarci wurin taron..