A Kano: Masu gidajen-kallo sun koma karkashin hukumar yawon bude-ido -In ji Sharu

A Kano: Masu gidajen-kallo sun koma karkashin hukumar yawon bude-ido -In ji Sharu

Gidan-kallo

Tura wannan Sakon

Daga Zainab Sani Shehu Kiru

Shugabancin kungiyar masu gidan kallo ta jihar Kano ta sanar da ficewar daga karkashin kungiyar tace fina-finai ta jihar Kano.

A wani taro da kungiyar ta shirya wa ya’yanta a ranar Litinin a gidan kallo na Lahai da ke kan titin Abdullahi Bayero, shugaban kungiyar na jihar Kano Sharu Rabiu Ahlan ya ce, sabuwar doka ce da hukumar bude ido da yawan shakatawa ta jihar ta ambaci gidajen kallon karara a cikin kulawarta, wanda hakan ya nuna cewa, gidajen kallon sun bar karkashin kulawar hukumar tace fina-finai, Sharu ya kara da cewa, daga yanzu duk masu gidajen kallon za su mayar da lamarinsu ne zuwa hukumar ta yawon bude ido, abin da ya ce, hakan wata dama ce da za ta kara inganta al’amura da samun daidaito na gudanar da sana’ar.

Dan gane da wani sako hukumar ta ce fina-finai take aikawa masu gidajen kallo inda suke umartarsu da su biya wadansu kudade, Sharu Rabiu ya ce, su dakata har sai abin da kungiya ta umarcesu ,

Daga karshe, Sharu ya yaba da irin goyan bayan da gwamna Abdullahi Umar Ganduje yake bai wa kungiyar ya ce, ya zama wajibi kungiyar ta yaba wa gwamnati tare da bin dokoki da gwamnati ke bijirowa da su musamman sabuwar dokar da ta dauke su daga karkashin hukumar tace fina-finai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *