A Kano: Masu sayar da manja, mangyada sun rage farashi’

Tura wannan Sakon

Daga Ahmad S. Ahmad

Shugabancin kungiyar masu sayar da manja da mangyada na kasa reshen kasuwar Galadima karkashin jagorancin Alhaji Muhammad Wada Yahaya sun tabbatar da samun raguwar farashin manja da mangyada, wanda a baya farashin ya kai Naira dubu 23, wanda a yanzu farashin yanzu ba ya haura 19 zuwa dubu 20.

Alhaji Muhahammad wada ya kara da cewa, suna bakin kokarinsu wajan ganin ba’a gurbata man da ake sayarwa a kasuwar kasancewar suna aiki tare da hukumomin tsabta da kuma na NAFDAC.

Da ake masa tambaya kan matsalolin da ake samu a hanyar su ta safarar kawo kaya daga wadansu jihohin kuwa, Alhaji Wada ya bayyana cewa, matsalar ce da ta addabi duk masu safarar kaya ta harajin kan hanya wanda a baya idan suka biya na dauko kaya guda daya sun gama, amma yanzu sai sun biya na kowacce jiha.

Daga karshe, ya nemi dukkan abokan huldarsudomin samun nasarorin da suka kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *