A Kano: Rangadin hukumomin tsaro, tabbatar da hadin-kai

A Kano: Gwamnati ta yi alkawarin kulawa da marayu

A Kano: Gwamnati ta yi alkawarin kulawa da marayu

Tura wannan Sakon

Zagayan da hukumoni tsaro ke yi da suka hada da Sojoji, Yansanda, Bijilanti, Hisbah, NDLEA da sauran ,a wasu unguwannin musamman a cikin kwaryar birnin Kano, ya nuna suna da kyakkyawan fahimta da kuma hadin kai tsakanin su.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin babban kwamandan Bijilante na jihar Kano, Alhaji Shehu Muhammad Rabi’u, alokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala wani zagayen hadin gwiwa da suka gudanar ana gobe babban Sallah.

Shehu Nuhammad Rabi’u, ya ce matukar ana bukatar tsaro a wani wuri a jihar a shirye suke su dakileshi.Kwamandan  ya ba da misali da yadda hukumomin tsaron suka sanya tsaro musamman alokutan shagulgulan karamar Sallah aka yi lafiya aka kuma tsahi lafiya batare da wata matsala ba , haka kuma babbar sallah da ta gabata an yi lafiya an tashi lafiya.

Ya kuma godewa gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje akan hadin kan da yake baiwa hukumomin tsaron jihar . Ya yi amfani da wannan dama da kira ga iyayen yara da su rika kula sosai da yaran su tare da sanin wadanda  suke hulda da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *