A Kano: Salka Media ta rarraba wa marayu 650 tufafin sallah

Salka Media ta rarraba wa marayu 650 tufafin sallah

Salka Media ta rarraba wa marayu 650 tufafin sallah

Tura wannan Sakon

Daga Ahmad S Ahmad

A karshen makon da ya gabata ne wadansu marayu suka rabauta da kayan sallah wanda Gidauniyar Salka Media ta ba su domin su ma a dama da su a yayin bukuwan salla karama mai zuwa.

Shugaban Gidauniyarkuma dan jarida, Sani Ahmad Sagagi ya bayyana wa manema labarai cewa, sun bayar da kayan ne dominsanya farin ciki ga yaran da kuma iyayensu, ta yadda za su yi bikin sallah a walwala.

Haka kuma ya kara da cewa, a cikin watan Fabrairu da ya gabata Gidauniyar ta yi wa marayu 69 kaciya tare da bai wa kowanne kaza guda daya da kuma magunguna har da kayan fitowa bayan warkewarsu, za kuma a tallafa masu wajen neman iliminsu gwargwadon abin da ya samu.

Da ya koma ta kan irin ayyukan Gidauniyar kuwa, ya bayyana cewa, suna horar da mata da matasa sana’o in dogaro da kai, tare da marayu da iyayensu. Sani Ahmad Sagagi ya kuma cewa, suna da rassancibiyar a kananan hukumomin Ungogo da Madobi da kuma Dambatta bayan babbbar cibiyar da ke cikinbirnin Kano.

Daga karshe, ya gode wamahalarta taron rabon kayan, ya kuma nemi wadan da suka amfana kan su tabbata sun za mo jakadun Gidauniyar nagari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *