A Kano: Shugaban kwalejin kimiyya ya kama aiki

Daga Jabiru Hassan
Sabon shugaban hukumar kula da makarantun gaba da sakandire na jihar Kano “Rector, Kano state Polytechnic” Dokta Kabir Bello Dungurawa ya kama aiki tare da yin alwashin kawo ingantaccen ci gaba a dukkanin makarantun dake karkashin wannan hukuma.
A jawabin sa yayin kama aiki a ofishin sa, Dokta Kabir Bello Dungurawa yace, da yardar Allah zai yi kokari wajen biniro da abubuwa masu amfani ga makarantun dake karkashin ikon hukumar ta yadda za’a ci gaba da samun yanayi mai gamsarwa na koyo da koyarwa bisa la’akari da shirin gwamnatin jihar kano wajen bunkasa ilimi a jihar.
Dokta Kabir Bello ya kuma nunar da cewa, ko shakka babu sha’anin ilimi yana samun ci gaba mai kyau idan aka dubi irin hidimar da gwamnan jihar ta Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ke kara vullo da kyawawan hanyoyi na kyautata wannan fanni ba tare da nuna kasala ba, wanda kuma hakan yana taimaka wa wajen samar da al’uma tagari.
Dokta Dungurawa ya kuma sanar da cewa zaiyi aiki kan wadansu manufofi guda bakwai wadanda za su zamo tamkar jagora wajen tafiyar da wannan hukumar ta kula da makarantu manya a jihar Kano wadanda suka hada da bude kofa ga kowa domin a hadu a yi aikin bunkasa ilimi da tabbatar da cewa, ana faranta wa malamai da daukacin ma’aikata da ke aiki a hukumar da kuma kyautata yanayin koyo da koyar wa.
Sannan ya ce, zai tsaya tsayin daka wajen ganin harkar kula da karatun dalubai tana tafiya daidai ta yadda za’a rika hanzarta duba aiyukan su na karatu, kana zai yi kokarin samar da karin hadin kai da fahimtar juna tsakanin hukumar da kungiyoyin dalibai, tare da inganta da’a tsakanin dalibai da malamansu ta yadda za’a kara samun ladabi a sha’anin karatu.
A karshe, Dokta Kabir Bello Dungurawa yayi amfani da wannan dama inda ya jinjinawa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje saboda nada shi da ya yi a matsayin shugaban hukumar kula da makatantun gaba da sakandire domin ya bada gusummawar sa wajen ci gaba ilimi a jihar Kano, tareda yin godiya da bangajiya ga dulkanin yan uwa da abokan arziki da abokan aiki bisa rakiyar da aka yi masa zuwa Sabon gurin aikin sa.