A Kano: SON ta jagoranci karrama kamfanoni

Daga Muhammad Mustapha
Nagartar kayayyakin da ake sarrafawa a Nijeriya za su iya yin gogayya da na takwarorinsu gida da waje.
Furicin ya fito ne daga bakin shugaban hukumar kula da nagartar kayayyakin da masana’antu ke sarrafa su a cikin gida, mai kula da shiyar arewa maso yamma, Alhaji Yunusa B Muhammad a lokacin wani bikin karrama kamfanonin da suka yi zarra a jihar.
Bikin wanda aka gudanar a otal na Ni’ima da ke Kano, inda ya kara da cewa, manufar karrama kamfanonin ita ce, bunkasa tattalin arzikin kasa da karfafa gwiwar masu masana’antu su cim ma ka’idojin cinikayya.
Ya ce, daga yau mun ba su wannan lambar girmamawan ba shikenan ba mun daina bibiyar ayyukan su, za mu ci gaba da bibiya har sai mun gamsu da yadda suke gabatarwa ta hanyar rike mana amana da suka yi, su ci gaba da samar da kayayyaki masu inganci kamar yadda suke kafin mu ba su shaidar girmamawar, idan kuma aka samu akasin haka kamfani ya canza tsarin ingancin kayansa za mu yi bincike idan laifin karami ne za mu ce ya gyara, idan kuma babba ne zamu karbe lambar girmamawar da muka bai wa kowanne irin kamfani ne, tare da shelanta wa duniya mun kwace shaidar girmamawar da muka ba shi, domin jama’a su sani.
A nasa bangaren, daya daga cikin wakilan kamfanonin da suka sami lambar girmamawar daga kamfanin Salam Bakery mai suna Malam Aminu Abubakar cewa ya yi, gaskiya wannan ba karamin abin da za a gode wa Allah ba ne la’akari da irin kamfanonin da suke a fadin jihar Kano amma a ce wannan hukuma mai albarka ta zabi kamfaninmu ta karrama shi a gaskiya mun ji dadi kuma muna yi wa Allah godiya, domin mun san bayan kokarin kamfaninmu da kwarewar mu akwai taimako na Allah, kuma ina da tabbacin cewa, duk kamfanin da aka ba shi wannan lambar girmamawa to ya cancanta, la’akari da yawan kamfanoni da suke a jihar.
Shi ma wakilin kamfanin Hill of Wealth Organization, Malam Umar ya ce, suna matukar godiya ga Standard Organization of Nijeriya bisa ga yadda ta zakulo su ta ba su lamabar girmamawar, tun da mu kamfaninmu harkar ruwa yake, mun san an duba ingancin ruwan mu ne aka ba mu wannan lambar girmamawar, ba wai saboda mun fi kowa ba, sai dai saboda mun sa ni kamfaninmu na daya daga cikin kamfanoni masu samar da ruwa mai inganci.
Wadansu daga cikin kamfanonin da suka samu lambar girmamawar sun hada da kamfanin Aspira Nigeria Limited da kamfanin Popular Farm and Mills Limited da kamfanin Jafa Form Product Nigeria Limited da ABY Lubricant Limited da kuma Salam Bakery and Catering Serbices.
Sauran sun hada da kamfanin Royal Foam Product Limited da kamfanin Hills of Wealth Inbestment da kamfanin Alyuma fertilizer and chemical limited da kuma kamfanin Authentic global enterprises limited.
Ragowar su ne, kamfanin Big Treat Plc da kamfanin Wayakan Nigeria Enterprises da kamfanin Joemabiz Nigeria Limited da kamfanin Royal Foam Product Limited sai kamfanin Gold Foam and Chemical industries limited.