A Kano : Za a horar da matasa 4,800 kan harkar tsaro

Daga Usman Usman Garba
Domin samar da ingantaccen tsarin tsaro a daukacin jihar Kano, gwamnatin jihar karkashin jagotancin gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ta yi alkawarin horar da matasa 4,800 daga kananan hukumomi 44 dake fadin jihar, kan yadda zasu kware a kan harkar tsaro.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye matasan da aka horas da kuma maraba da sababbin dauka na makarantar koyar da harkokin tsaro watau, (Kano state Corporate Security Institute) dake karamar hukumar Gabasawa.
Daga cikin 4,800 da ake shirin horarwa, kowace karamar hukuma dake kwaryar birnin Kano za ta bayar da mutum 150 , sai kuma sauran kananan hukumomi na wajen birni da za su bayar da mutum 100 kowannensu, a cewar gwamnan.
Gwamnan ya kara da cewa, “Ya kamata mu tashi tsaye mu tabbatar da cewa mun sa dukkan hannayenmu wajen tabbatar da tsaro a Kano da kuma kasa baki daya.”
“Baya ga matasa 4,800 da za a horar da su daga kananan hukumomi 44, za a kuma horar da sama da ma’aikata 5,000 na Hukumar Kula da sifuri ta jiha watau (KAROTA) a wannan Cibiyar. Muna yin hakan ne don inganta ayyukanmu a cikin al’umma, da kuma ganin tsaro ya tabbata.” a cewar gwamnan
A nasa jawabin Darakta Janar na Makarantar, (Mai Ritaya) Mataimakin Kwanturola na Hukumar Shige da Fice, Isma’ila Tanko Wudilawa, ya yaba wa gwamnatin jihar kan jajircewarta wajen tabbatar da tsaron al’umma.
Ya kuma yaba wa gwamnan bisa jajircewarsa wajen ganin makarantar ta bunkasa, inda ya yi alkawarin cewa makarantar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin nasarar matasan da take horarwa kan harkokin tsaro.