A Kano: Zuwan Ezone zai bunkasa kasuwanci -Hamisu Rabiu

A Kano: Zuwan Ezone zai bunkasa kasuwanci

Zuwan Ezone zai bunkasa kasuwanci

Tura wannan Sakon

Daga Ibrahim A. Muhammad

An bayyana cewa, ji­har Kano cibiya ce ta kasuwanci da kam­fanoni ke zuwa daga wurare daban daban daban dan kara huldar kasuwanci.Alhaji Yu­suf Salisu Gidan Gado dan kasuwa da yake hulda da ka­mfanin “EZONE”ya bayyana haka yayin bude reshen kan­tin zamani na Saida kayayya­kinsu a Kano.

Yace arzikine daya zowa Kano dazai taimaka wajen samarda aikinyi dazai dada bunkasa tattalin arziki da yake da a Legas kamfanin yake sakamakon mu’amala da suke dashi sukaga cewa da amfani daya kamata Kano ta amfana sukayi kokarin jawosu Jahar Kano dan gina Kasuw­anci azo a kafa masana’anta a samarda aikinyi da mutane zasu amfana.

Yace wannan cigaba da ake samu yana nuna Kano na havaka a Kasuwanci tareda tafiya da zamani Kasuwancin­da ake yanzu na tafiya da za­mani da ba’a irin wannan Ka­suwanci ayi “showroom” sai dai aje a sai kaya da aka kasa a kasuwa kamar gyada to amma yanzu anzo da “showroom”Ba kayanda ba’a samu.

Alhaji Yusuf yace dangan­takarsa da kamfanin EZONE abokin huldarsune a Kano Kuma suna abubuwa tare ta mu’amila ta shekaru da yawa. kuma fatansu wannan ya Zama sila ta cigaba da bude wasu da dama.Burinsa inda hali duk wani wajen suje su sanya hulda ta Kasuwanci ya fadada a sami aikinyi ga al’ummar Kano.

Alhaji Yusuf Salisu yace sun jawo kamfanin ne view hange na yanda Kano take da zaman tafiya su Kuma bisa sha’awarsu rasa Kasuwanci a Kano amma suna fargaba suka tabbatar musu ba wani abu sukazo da zimmar gwaji sukazo sukaga zahiri sannan daga baya sukazo suka dauko za susa dukiyarsu anan, da tsura sukazo suzo su gani abi­nda suka fada gaskiyane sun gani sun gamsu.

Gidan gado ya sharwarci yan kasuwa a Kano suyi am­fani da irin wannan dama tayin mu’amala da irin wan­nan kamfanoni Wanda kay­ansu robane daidai da wan­don kowa daidai kudi daidai shagali.

Shima wani fitaccen dan kasuwa a Kano.Shugaban “Hamir Investment”Alhaji Hamisu Rabiu yace wasu irin wasu kayayyakin sai a wajen kasarnan ko Legas yanzu sunzo Kano Kuma Kasuw­anci kayayyakin masu saukin Kaine da sassautawa sunyi farin ciki da samun wannan cigaba wannan arzikine da mutane da yawa zasu mora.

Alhaji Hamisu Rabiu ya kara da cewa yace yanzu har­koki sun Kuma a zamanance Kuma ta hadu da yan zamani anyiwa waje kwalliya da in mutum yazo zaiji farin ciki. Kuma sunzo da abinda ka­suwa ke bukata na sauki da inganci Kuma zuwansu sai haifarda alkhairi.Suna fata kafin karshen shekaru a sami karin wasu da yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *