A Kano:Mutane 113 sun amfana da tallafin gidauniyar AlKamat

A Kano:Mutane 113 sun amfana da tallafin gidauniyar AlKamat
Kimanin matasa 113 ne suka sami tallafin kuDi Naira milyan biyu kowannen su wanda gidaunyar Alkamat Brains BoD a jahar Kano domin inganta harkokin kasuwancinsu.
Hakan na zuwa ne daga bakin shugaban gidauniyar Alkamatu Hussaini wanda ya bayyana wa manema labarai jim kaDan bayan kammala taron Kara wayar wa da al’umma kai kan mahimmancin riKe sana’a komai KanKantar ta. Alkamatu Hussaini ya kuma bayyana cewa kada mutum ya sami kasawa a duk lokacin da ya sa wani abu a gabansa mutuKar abin zai kawo masa ci gaba ne na rayuwa.
Haka kuma matashin mai kimanin shekaru ashirin da bakwai ya ce, lallai lokacin da yake neman wannan tallafi daga gidauniyar Tony Elumelu sai da ya jarabba a lokuta da yawa kafin cim ma nasara. Ya ce, ya zuwa yanzu babu abin da zai ce sai godiya ga Allah da ya ba su nasara na samun wannan abu da yanzu haka suka tabbatar wa al’umma nagarta da jajircewa wajen neman na-kai.
Shugaban Kungiyar ya kuma jinjina wa shugaban Dakin karatu na jahar Kano, ta yadda ya zaburar da shi tare da zama uba a gare shi da jan linzaminsa lokacin neman wannan kuDaDe. Kazalika ya hori waDanda suka sami tallafin da su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace wajen mayar da hankali ga abin da suka yi alKawarin za su yi da su, sannan kuma ya Kara horar su da su ma idan sun sami dama su taimaki wasu al’umma domin fita daga Kangin babu. Ya kuma ce, lallai kasancewar suna buKatar Kano ta zama kan gaba wajen harkar kasuwanci sun shirya tsaf wajen ganin sun taimaki jama’ar da suke da muradin kasuwanci a jihar Kano.
Dokta Samuel Adebayo ya bai wa waDanda suka amfana da tallafin shawarwarin yadda ya kamata su fara kasuwanci tun daga matakin farko bawai sai ya tara kuDaDe masu yawa ba. Samuel ya ce, kamata ya yi mutum ya duba menene al’umma suke buKata tare da kawo shi a kasuwa, inda ya Kara da cewa, Dankasuwa ya kasance mai fara’a da iya tarairayar masu sayen kaya