A karo na farko: Senegal ta lashe kofin Afirka

Tura wannan Sakon

Kasar Senegal ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta Afrika Acon ta shekarar 2021 An shafe mintuna 120 ana fafatawa ba tare da an samu wanda ya ci a fili ba, har sai da aka kai bugun daga kai sai mai tsaron gida A nan ne Senegal ta doke Masar da ci 4 da 2. An fara gasar ne da kungiyoyi 24, kafin a gangaro zuwa kasashe biyu da suka buga wasan karshen a yanzu.

Masar ta rasa damarta ta daukar kofin karo na 8, inda ita kuma Senegal ta dauki kofin a karon farko Tun a zagayen farko Sadio Mane, wanda aka zuba wa ido a kansa a bangaren dan wasan Liberpool ya kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron gida da kasarsa ta samu, wani abu da ya rage kwarin guiwar dan wasan da farko.

Golan Masar Gabaski ya yi namijin kokari ta hanyar ture kwallaye da dama da aka rinka buga masa, ciki har da ture kwallo daya a bugun daga kai sai mai tsaron gida, abun da ya sa aka ba shi golan da ya fi taka rawa a wasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top