A Katagum: Kwamitin tsaro ya katse hanzarin dillalan kwayoyi

Tsaro: Kaura ya jagoranci taron gaggawa
Tura wannan Sakon

Sani Gazas Chinade Daga Azare

Masarautar Katagum a jihar Bauchi a karkashin Mai martaba Sarki, Alhaji Umar Faruk Kabir 11 ta kafa kwamiti mai karfin gaske karkashin jagorancin magajin Ali Kwara, Alhaji Ahmed Mohammed, domin yaki da masu sayar da miyagun kwayoyi da tabar wiwi da matasa ‘yansara-suka.

Kwamitin ya yi nasarar damke manyan dillalan tabar wiwi da sauran kayayyakin sanya maye 11 da ke masarautar Katagum.

A wani samame da kwamitin tsaro ya kai a sassa da dama na masarautar karkashin Jarmai Unkuji da hadin gwiwar jami’an ‘yan-sanda sun sami nasarar cafke dillalan tare da tulin kayayyakin sa maye wadanda aka shigo da su cikin masarautar.

Wadansu daga cikin miyagun kayayyakin da aka kama sun hada da tabar wiwi da kwalaben maganin tari na Fakalin da kwayar maganin Baliyon Dzol wadanda kudadensu ya haura Naira miliyan 20 wanda tuni har sun sayar da na Naira miliyan 19 daga ciki.

Bincike ya nuna cewa, babban dillalin da yake da kayayyakin ya fito ne daga garin Chinade, cikin karamar hukumar Katagum, a yayin da dan achaban da ake bayarwa domin shigo da kayayyakin garin Azare shi kuma dan kauyen Gangai. Shi kuma babban dilan da ake kawo wa kayayyakin mai suna Dan Malam dan garin Azare ne, yadda shi kuma yake rarraba su ga abokan harkokinsu.

Bayan da aka gabatar da dillalan kayayyakin ga Mai Martaba Sarkin Katagum, nan da nan jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) suka tasa keyarsu zuwa garin Bauchi babban ofishin hukumar domin fuskantar laifinsu.

A cikin jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Katagum, Alhaji Umar Faruk Kabir 11 ya ja kunnen iyayen yara da su rinka sanya ido kan ‘ya’yansu musamman irin mutanen da suke hulda da su. Mai Martaba Sarkin ya kuma yaba wa kwamitin bisa aikin sa-kai da suke yi domin daidaita sahun matasan yankin. Ya kuma yi addu’ar Allah ya bayar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Katagum da jihar Bauchi da ma kasa baki daya.

Wannan aiki da kwamitin tsaron ke yi na kara faranta ran al’ummar masarautar musamman mazauna garin Azare da a kullum lamarin tsaro sai kara sukurkucewa yake yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top