A Katsina: APC ta yi zaben shugabanni ta hanyar sasanci

A Katsina: Shirin basda ya inganta ilimi a jihar

A Katsina: Shirin basda ya inganta ilimi a jihar

Tura wannan Sakon

Isma’il Usman Daga Katsina

Jam’iyyar APC a ji­har Katsina ta yi za­man sasanci da zum­mar yin zaben sababbin shugabanni da nufin dinke baraka tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

Shugaban Ma’aikata a ofishin gwamna, Alhaji Muntari ya ce, a dukkan tarurruka da aka yi a fadin jihar jam’iyyar ta yi na­sara.

A Cewar sa, masu sharhi sun tabbatar duk fadin kasar nan babu inda aka yi sahihin zabe na fa­himta kamar jihar Katsina.

Shugaban ma’aikatan ya kara da cewa, nasarar ta samu ne a sakamakon irin kulawa da adalci da gwamna yake yi wa ‘yan ‘yan jam’iyyar a jihar.

Kuma dukkan ‘yan jam’iyyar sun bayar da hadin kai da goyon baya dari bisa dari, wannan ala­ma ce ta ‘yan APC na gas­kiya. Kuma tabbas tun da aka fara tafiyar babu inda aka samu sabanin fahimta balle wani nau’i na tashin hankali.

Alhaji Muntari Lawal ya yi jan hankali da cewa, duk wanda ya ga an yi masa abin da bai yi masa daidai ba, cikin natsuwa da kwan­ciyar hankali ya gabatar da bukatar sa ko koken sa do­min a bincika a yi abin da ya kamata domin warware zare daga abawarsa cikin lumana.

A taron zaben shuga­bannin jam’iyyar wanda ya gudana ranar Asabar 16/10/2021 shugaban kwamitin tsare tsaren zaben kuma shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin hijar Katsina, Alhaji Muntari La­wal ya yi jawabin godiya ta musamman ga gwamna da ya basu damar gudanar da gagarumin aikin na aiwatar da Zaben tun daga matakin Mazabu har kananan huku­momi da kuma jiha.

Daga cikin wadanda aka zaba akwai Alhajhi Sani Aliyu Daura a matsay­in shugaba, Bala Abubakar Musawa a matsayin Ma­taimakin shugaba, Shitu S Shitu sakatare sai kuma Umar S Mustafa mataima­kin sakatare da Babangida Yardaje a matsayin ma’aji da sauransu.

A jawabin gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi kira ga sabab­bin shugabannin da su zama tsintsiya madaurin ki daya sannan za su samu nasarar tafiyar da nauyin da aka dora masu na shugabancin jam’iyyar.

Ya fadi haka ne a yayin gudanar da zaben ta hanyar sasanci a Muhammadu Dik­ko Stadium Katsina.

Gwamnan ya yaba ma kwamitin gudanar da za­ben tun daga na mazabu da kananan hukumomi da kuma na jiha da aka yi a ranar, musamman shugaban kwamitin, Alhaji Muntari da abokan aikin sa da suka dage ba dare ba rana, do­min ganin an samu nasarar ayyukan.

Haka kuma gwamnan ya yi godiya ta musamman ga dukkan magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Kat­sina da kasa baki daya.

Daga karshe, sabon shugaban jam’iyyar ya yi jawabin godiya a tare da tabbatar da cewa, za su yi aiki bisa adalci kamar yad­da ya kamata.

Taron ya samu halar­cin jiga-jigan jam’iyyar da suka hada da KS Alhaji Mannir Yakubu, matai­makin gwamna da Sanata Hadi Sirika da Alhaji Tasi’u Maigari da Alhaji Ahmad Dangiwa sai kuma Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da Injiniya Surajo Yazid Abu­kur MD Kasroma da Al­haji Mustafa Muhammad Inuwa Sakataren gwamnati da manyan ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da matasa sun shaida cancantar sababin zababbun shugabanin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *