A Katsina: Hukumar ilimi bai-daya ta bayyana nasarorinta -Buhari Daura

A Katsina: Shirin basda ya inganta ilimi a jihar

A Katsina: Shirin basda ya inganta ilimi a jihar

Tura wannan Sakon

Isma’il Usman Daga Katsina

Daga cikin ci gaban da aka samu ta fanin ilimin firamare da karamar sakandare a jihar Katsina in ji Alhaji Lawal Buhari Daura shugaban hukumar ilimin bai daya, daga shekarar 2015 da suka hau shugabancin jiha dukkan duk ginin sabuwar makaranta ko kuma gyara daga shekara 2016 zuwa yanzu akwai alamomi na fenti kala biyu fari da bulu mai nuna alamar jam’iyyar APC ce ta yi aikin, gwamna Aminu Bello ya ce, baya son ya ga wani sabon gini ko gyara na makarantu ba tare da an sa masu tebura da kujerin zama yadda za a samu kyakkyawan yanayin koyo da koyar wa ba.

A haka muka ci gaba da tafiya bisa tsarin duk makarantun da muka gina ko muka gyara sai an sanya kujeri da tebura, a da can mafi yawan makarantu babu wutar lantarki amma yanzu kowace a kan hada wayoyin lantarki a kowane aji da ofisoshi kuma a sa injin samar da hasken wutar janareta domin kyautata yanayin aiki.

 Haka nan masu bukata ta musamman ba a bar su a baya ba, saboda masu kowane nau’i na nakasa an kyautata yanayin koyo da koyarwar su abin da ya shafi karatu da rubutu da tsarin hanyoyi da gini na ajujuwansu.

Maganar karin girma ga malamai kuwa rabon su da wannan tun a shekarar 2012 a lokaci gwamnatin da ta wuce.

Zuwan gwamna Aminu Bello Masari Dallatun Katsina mun yi kokarin kau da matsalar, duk malaman da suka cancanci karin girma an yi masu, hakan kuma ya kara zaburar da su ga ayyukansu an kuma ba su bashin baburan hawa ga masu bukata, domin samun damar kasancewa a wuraren ayyukansu kan lokaci.

Maganar daukar ma’aikata kuwa mun dauki malamai na dindindin, kuma gwamna Aminu Masari ya kwaikwayi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi Npower a matakin kasa, shi ma mai gwamna ya yi Spower a matakin jiha da nufin rage yawan marasa ayyukan yi a jihar .

      Za muci gaba a mako mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *