A Katsina: Ma’aikatan lafiya sun yi rawar gani -Sani Yusuf Saulawa

Ma’aikatan lafiya
Isma’il Usman Daga Katsina
A duk lokacin da aka tashi aiwatar da wani abin kirki a kan fuskanci kalubale nan da can koda yake manbobinmu na gudanar da ayyukansu yadda ya kamata suna sauraren mu kuma suna ba mu hadin kai hakan ne ya kasance a gare mu.
Ma’aikatan kula da lafiya na kokarin kasancewa bakin aikinsu yayin da muke kokarin tsare amanar da ke hannuwan mu domin tabbatar da kula da lafiyar jama’a, a cewar Kwamared Sani Yusuf Saulawa, sakataren kungiyar ma’aikatan lafiya a jihar Katsina.
Hakika al’umma sukan yi korafi dangane da tirjiya da ake samu a wadansu lokuta daga wadansu ma’aikatanmu, wannan yakan faru ne sakamakon karancin ma’aikata na dindin-din da ya kamata su kula da wurare da abubuwa daban-daban, domin haka muna jinjina wa ma’aikatan mu da suke ba mu goyon baya bisa mayar da hankali ga abin da ya kamata na tsare ayyukansu da tafiyar da su kan tsari gwargwadon iyawar su.
A Katsina muna da yawan jama’a ba su sani ba a nan shi ne kananan asibitoci da matsakaita da manya, akwai karancin ma’aikatan lafiya wadansu sun mutu wadansu sun ajiye aiki, gwamnati kuma tana kokarin cike guraben amma yawansu bai kai rabin rabin jama’ar da ya kamata a kula da su ba.
Mun san irin kokari da juriya da mambobinmu suke yi domin tsare ayyukansu na kula lafiyar al’umma. Idan aka yi la’akari da yawan mutanen da kan je neman lafiya a asibitoci yawan masu kula da su, ba su kai yawan marasa lafiyar ba ya dace a yi mana uzuri.
Kodayake an dauki tsawon lokaci ana fadakar da jama’a tsare tsare da kuma muhimmancin na wannan shirin kula da lafiyar jama’a wanda ma’aikata kan bayar da wani kaso daga cikin albashinsu.
Gwamnati ta bayar da wani abu da dama ba su fahimci muhimmanci da alfanun abin ba, shi yasa har zuwa yanzu suke fuskantar matsala duk lokaci idan sabon abu ya zo sai a hankali za a fahimce a saba da shi, mafi yawan koken da muke samu mutum ya ce, bai samu katinsa ba .
Mun sha fada masu su je wuraren da suka yi rajista suka bayar da sunan su daadireshi, nan take za a bincika a fitar da mutum katinsa sai dai in ya yi kuskure ne lokacin daya cike fom din nasa ko kuma katin ne ya bace ko mutum naso a yi masa canjin asibiti har hakan ma idan aka bi a hankali za a warware kowace irin matsala ce.