A Katsina: Nagge-dadigoma ta rarraba litttafai dubu 280

Kin mallakar makamin kare kai, kuskure –Masari

Governor Masari

Tura wannan Sakon

Daga Muawuya Bala Idris, Katsina

Gidauniya Nagge-dadi-goma ta bayar da gundunmar littatafai na rubutu guda dubu 280,000 ga makarantun firamare a jihar Katsina.

Shugaban zartarwa na Gidauniyar, Alhaji Babangida Inuwa shi ya mika littatafan ga gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari. Inuwa ya ce, littattafan rubutun za a yi amfani da su ga ‘yan aji biyar na firamare domin taimaka masu wajen bunkasa iliminsu.

Ya ce, gidauniyar ta bayar da lit-tatafan bayan nazari da irin bukatar da makarantu da dalibai suke bukata na samar da kayayyakin koyarwa. Inuwa ya ce, gidauniyar wacce aka kafa shekaru 3 da suka gabata, tana da kudurin ta hada hannu da gwamanti wajen magance matsalolin da ke addabar jihar.

Ya ci gaba da cewa, gidauniya ta shirya tsaf domin koya wa matasa kusan 900 sana’ar hannu domin dogaro da kai. Haka kuma, gidauniya tana hadin gwiwa da hukumar sha da fataucin kwayoyi wajen magance mu’amulla da kwayoyi a cikin matasa. Inuwa ya bayyana cewa, gidauniya ta fara samar da ruwan sha ta hanyar gina rijiyoyi a fadin jihar.

Da yake mayar da jawabi, gwamna Masari ya yaba wa gidauniyar wajen hada kai da gwamnati domin magance matsalolin da jihar ke fuskanta. Masari ya hori ma’aikatar ilimi ta tabbatar da yin amfani da littatafan domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *