A Katsina: NUJ ta karrama gwamna Masari

Tura wannan Sakon

Daga Isma’il Usman Katsina

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Katsina ta himmatu matuka domin ta inganta yanayin sakatariyar kungiyar fiye da tunanin jama’a saboda samar da kyakkyawan yanayi ga ‘yan jarida ta yadda za su fadakar da ilimantar da sauke nauyin al’umma ta hanyoyin da suke gudanar da ayyukansu na jarida.

Wannan yana daga cikin dalilai da ya sa gwamna Aminu Bello Masari ya yi wani yunkuri na musamman bisa ga kokarin kungiyar NUJ ta jihar Katsina karkashin jagorancin Kwamred Tukur Hassan Dan Ali .

Kasantuwar gwamna Aminu Masari tsohon ma’aikacin da ya yi gwagwarmayar iri daban-daban a wurare da suka taimaka wa ci gaban al’umma ta fannin aikin gwamnati da harkokin siyasa a kasa baki daya.

Gwamna Masari ya san muhimmancin aikin jarida kuma ya yi hulda da ‘yan jarida kwarai da gaske.

Kwamred Tukur Dan Ali ya ce, gwamna ya bayar da tallafin da kungiyar ta gina manyan runfuna na zamani guda biyar, a tsakiyar filin da fanfunan suka zagaye an yi wuraren wasanni kala uku da suka hada da kwallon badminton da kwallon tebur da kwallon zungure a cikin farfajiyar sakatariyar da ke cikin unguwar Lay Out ta kofar Kaura.

Duk shekara NUJ Katsina ta kan yi liyafar cin abincin dare a zagayowar ranar ‘yan jarida ta duniya, Kwamred ya ce, shekarar 2021 ba mu yi ba saboda mun tanadi wadansu abubuwan da muke bukatar zartas da su lokaci daya.

Hakan ne yasa ranar Li

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *