A Katsina: PRP ta ja damarar lashe zabe

Daga Muawuya Bala Idris,
Katsina Jamiyyar PRP a jihar Katsina ta kafa kwamitin yakin nenan zabe mai mutane 120.
Jamiyyar ta zabi Dokta Usman Bugaje ya zama shugaban kwamitin. Da yake magana da manema labarai, babban darakta na kwamitin, Dokta Magaji Aliyu Dansarai ya ce, an zabi tsohon shugaban ma’ikatan jihar Katsina, Abdulrahman Abdullah ya zama daya daga cikin ‘yan kwamitin. Dansarai ya ce, ‘yan kwamitin an zabe su bisa chanchanta da kwarewar aiki.
Ya ce, tuni jam’iyyar PRP ta jihar ta fitar da manofinta domin samun nasarar zabe. Ya kara da cewa, jam’iyyar ta tsayar da mutane masu gaskiya da rikon amana a matsayin ‘yan takara.
Ya ce, burin jam’iyyar PRP shi ne ta kawo ci gaba tare da magance matsalolin da ke addabar jihar.
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar na jihaHassan Hamisu ya karyata cewa, magoya bayan jam’iyyar a jihar Katsina sun koma APC.
Hamisu ya ce, ba wani dan PRP da ya koma watai jamiyya a jihar.
Ya ce, wani Ahmed Hassan wanda yake kiran kansa da sunan shugaban jam’iyyar ba dan jamiyyar PRP ba ne.
Hamisu ya gargadi Ahmed Hassan ya daina amfani da sunan jam’iyyar ko ya fuskanci tuhumar kotu.
A nasa bangaren, dan takara gwamna na jam’iyyar, Imrana Jino ya kalubanci ‘yan takarar gwamna nasauran jam’iyyu da gudanar da muhawara a tsakaninsu.
Jino ya ce, zai taimaki mutanen jihar wajen zabo shugaban mai inganci wanda ya dace da ya jagoranci jihar.